kungiyoyin Yaki da Cin Hanci da Rashawa Sun yi Watsi da karar da Abba Kyari
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ranar Laraba, ta sanya ranar 10 ga watan Fabrairu domin sauraren karar da ke neman dakatar da rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, kama tare da mika mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari.
Punch ta rawaito, mai shari’a Donatus Okorowo, ta tsayar da ranar ne biyo bayan rashin halartar mai shigar da kara, da Incorporated Trustees na Northern Peace Foundation da wadanda ake tuhuma guda biyu, NPF da AGF, a kotu.
Best Seller Channel
Duk da cewa an shirya gabatar da karar ne a gaban wani sabon alkali mai shari’a Okorowo, babu daya daga cikinsu da suka halarci kotun, haka kuma ba su samu wakilcin masu shari’a ba.
Jim kadan bayan shigar da karar babu wani lauya da ya sanar da bayyanar da wanda ake kara da wadanda ake kara, alkalin kotun ta tambayi magatakardar kotun ko wanene wanda ya shigar da karar, aka shaida masa Kayode Ajulo.
Mai sharia ya ce tun bayan da aka mika karar zuwa kotunsa ba a kai wadanda ake kara ba saboda babu wata shaida a cikin bayanan kotun.
A cewarsa, ko dai mai nema ya rasa sha’awa a lamarin ko kuma ya yi watsi da shi.
Mai shari’a Okorowo, ya ce tun da maganar ta zo a karon farko a gabansa, ya gwammace ya baiwa wanda ake nema har zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu ya kasance a kotu domin ya gurfanar da shi gaban kuliya. Don haka ya bayar da umarnin a ba da sanarwar sauraren karar.
Best Seller Channel
A ranar 19 ga watan Agustan 2021 ne hukumar ta ITNPF ta shigar da karar a gaban kotun ta lauyoyin ta, karkashin jagorancin Ajulo, inda ta bukaci kotun da ta dakatar da duk wani shiri na kama Kyari ko mika shi kasar Amurka da wadanda ake kara ke shirin yi har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar da kuma yanke hukunci na karshe.
Sai dai bayan sauraren karar da lauyan mai shari’a Ahmed Mohammed da ke kan shari’ar a lokacin ya yi kunnen uwar shegu, ya ki amincewa da bukatar dakatar da tsare Kyari tare da mika shi ta hanyar da ta dace.
Best Seller Channel
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta gurfanar da Kyari bisa zargin zamba na miliyoyin naira da aka ce wani dan Najeriya, Ramon Olorunwa Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi ya aikata.