Da Dumi Duminsa! Shugaba Buhari Ya Bada Umarnin Cigaba Da Twitter A Nigeria

Shugaba Buhari Ya Bada Umarnin Cigaba Da Twitter A Nigeria  

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Shugaba Muhammadu Buhari ya dage dakatarwar da aka yi a shafin Twitter a kasar, daga karfe 12 na daren laraba, 13 ga watan Janairu, 2022. 

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Laraba mai dauke da sa hannun babban daraktan hukumar. 

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa kuma Shugaban Kwamitin Fasaha na Najeriya Twitter Engagement, Kashifu Abdullahi. 

Best Seller Channel 

Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurce ni da in sanar da jama’a cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da janye dakatarwar da aka yi wa kamfanin na Twitter a Najeriya daga karfe 12 na daren yau, 13 ga watan Janairu, 2022. 

Hakan. ya biyo bayan wata takarda da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital, Farfesa Isa Pantami ya rubuta wa Shugaban kasa.”

Slide Up
x