Kusan Mutane 14 Ake Fargabar Sun Mutu a Kano Sakamakon Shan Shayi A Wurin Biki

Alfijr ta rawaito wasu samari da dama sun mutu wasu kuma na kwance magashiyyan a asibitin sakamakon shan shayin da ake zargin an dafa shi da ganyen zaƙami a wurin wani biki a unguwar Sheka da ke birnin Kano.

Shaidun gani da ido sun shaida wa majiyar mu cewar akalla mutane 50 abin ya shafa.

Sunusi Yahaya, wanda yaya ne ga amarya, ya ce bayan dafa shayin da zaƙami, akwai muggan kwayoyi masu bugarwa ma da samarin suka zuba a cikin shayin kuma suka dafa da su.

Ya ƙara da cewa, yanzu abin ya zama ruwan dare ga matasa a yankin, a duk lokacin da suke biki, sai su dafa shayin da suke zuba masa muggan kwayoyi a ciki, su fake da shan shayi domin su yi shaye shaye.

” Saboda ƙarfin kwayoyin da yaran suke sakawa a shayin ta kai ta kawo wasu ma basa iya sha, wasu kuwa a hakan suke shanyewa wai ala dole sai sun bugar da kan su” in ji shi.

Yace tun a ranar bikin, nan take mutum biyu suka mutu bayan sun sha shayin.

Freedom Radio a nata rahoton ta bayyana cewa, izuwa yanzu mutane 14 ne suka mutu, kuma da dama suna kwance a asibiti.

Wasu ma ba yan unguwar bane, kawai sun zo wucewa ne suka ga ana shan shayin suka tsaya suka sha, daga nan kuma mai afkuwa ta afku.

Rahotanni sun ce angon ma ya ranta a na kare tare da wasu abokansa tun da abin ya faru.

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda na jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun nan sun fadada bincike kafin su magantu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *