Wata Mummunar Gobara Ta Tashi A Sansanin Sojojin Saman Najeriya Da Ke Abuja

Alfijr ta rawaito gobara ta kone sansanin sojojin saman Nijeriya.

Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar a sansanin sojin sama da ke kan titin filin jirgin ba, har zuwa lokacin da ake cike wannan rahoto.

A halin yanzu ana ci gaba da sa baki daga jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya domin kashe gobarar.

Shugaban ayyuka na FFF FCT, Amiola Adebayo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce jami’an kashe gobara na bakin kokarinsu wajen ganin an kashe gobarar gaba daya.

“Gobarar ta kone wani bangare na NAF Base, kuma mutanen mu suna nan suna kashe gobarar, kuma muna aiki tukuru don ganin an kashe gobarar gaba daya.

“Duk da haka, ba zan iya tabbatar da musabbabin barkewar gobarar ba tukuna, amma za mu fitar da sanarwa da zarar an kammala bincikenmu.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *