Wani ɗan majalisar wakilan Najeriya a jihar Kebbi ya aurar da ‘yan mata marayu guda 100 a wajen wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar ranar Asabar.
Alfijir Labarai ta rawaito an ɗaura wa marayu 100 auren ne a fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Ismail Muhammad, wanda ya jagoranci daurin auren.
An ɗaura auren ne ɗaya bayan ɗaya bayan sanar da biyan sadaki da kuma waliyyan kowane ango da amarya.
Kowace ɗaya daga cikin amaren ta samu kyaurar saitin gado da kujeri da sauran kayan ɗaki da kuma AlKur’ani mai girma.
Ɗaya daga cikin amaren Hafsat Ismail Haruna ta bayyana auren a matsayin wani babban al’amari ga rayuwarta.
“Wannan ba ƙaramin gata ba ne domin ban taɓa tunanin zan yi aure nan kusa ba saboda ban san uwa da uba ba,” in ji ta.
Ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Argungu/Augie a majalisar wakilai Hon Sani Yakubu Noma wanda ya ɗauki nauyin aurar da ‘yan matan har 100 ya ce ya san maraici, domin shi maraya ne, kuma wannan ne dalilin da ya sa ya jagoranci aurar da marayun.
Ɗan majalisar ya kafa kwamiti da suka jagoranci tabbatar da auren na marayu. Ya kuma ce zai ci gaba da aurar da marayun duk shekara tsawon wa’adin shekaru huɗu da zai yi a majalisar tarayya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp
Wannan lamari abun a yabane
Gaskiya mun yi murna sosai wllh. Mu ma sai mu taho Kebbi mu samu Amarya zuwa nan Gombe.
Allah Ya saka masa Ya kuma kara dafa masa da karin girman kujera. Allah sa kar ya taba kasa, ma’ana, har karshen rayuwarsa ya kasance cikin mulki mai albarka.