Labari Mai Dadi! Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Gana da Sheikh Daurawa

FB IMG 1709243391928

Akwai yiwuwar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya koma kan mukaminsa na kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano bayan ya gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf,

Alfijir labarai ta rawaito rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya gana da Sheikh Daurawa da wasu manyan jami’an hukumar Hisbah a sirrance a ranar Asabar.

A cewar mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah ta Kano Dr Mujahid Aminuddeen, Gwamna Abba Kabir ya yiwa jami’an Hisbah tare da Sheikh Daurawa bayani sosai kan dambarwar da ake yi.

“Mun yi taro da Sheikh Daurawa, inda aka warware duk wata matsala, kuma aka yi nasara a kan makircin da Shaidan ya shirya.

“Kano ta kasance kasa ce cibiya ce ta Addinin Musulunci tsawon shekaru, don haka ya kamata mu kiyaye ta ta hanyar yakar duk wani sharri da ke barazana ga addininmu da al’adunmu”.

Muna yin wannan aiki ne don Allah da kuma taimaka wa gwamna ya samu nasara. Jama’a za su ji labari mai dadi nan ba da jimawa ba,” in ji Dokta Aminuddeen a wani gajeren bidiyo .

Daily News 24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *