Labari Mai Dadi! Gwamnan Kano Ya Biya Kudin Rijistar Sabbin Daliban Jami’a 1,740

FB IMG 1715254046724

Gwamna Kano ya biya kudin rijistar sabbin dalibai 1,740 da suka samu gurbin karatu a jami’ar ilimi ta Saadatu Rimi da ke Kumbotso mallakin gwamnatin jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito Gwamna Abba ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin kammala karatun digiri na farko na makarantar.

A shekarar 2023 ne Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da sabunta Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso a Jihar Kano zuwa jami’ar ilimi.

Ya ce gwamnatin jihar ta himmatu sosai wajen tallafawa bukatun ilimin dalibai ba tare da la’akari da siyasa ba.

Ya ce gwamnatin jihar ta kuma ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kudinta na shekarar 2024 ga ilimi, wanda hakan ya nuna samu karin kan shekarun baya.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Dr Ibrahim Kofarmata ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yafe kashi 50 na kudaden makaranta na makarantun sakandire da manyan makarantun jihar domin samun saukin ilimi ga yara masu rauni.

Shugaban Shugaban Jami’ar Farfesa Yahaya Isa Bunkure, ya yabawa kwazon Gwamna Abba wajen bayar da ilimi tare da bayyana irin nasarorin da jami’ar ta samu, da suka hada da shirye-shiryen bunkasa ma’aikata, ayyukan bincike, da inganta ababen more rayuwa.

Bunkure ya ja kunnen daliban da suka kammala karatunsu da su himmatu da azama, tare da sanin muhimmancin zamansu a jami’ar.

Bunkure, ya kuma samu lambar yabo ta Fellowship daga Cibiyar Nigerian Institute of Physics (FNIP) saboda gudunmawar da ya bayar a fannin da jajircewarsa wajen bincike da ilimi.
(NAN)

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *