Labari Mai Dadi! Gwamnatin Kano Za Ta Yi Aiki Da Kasar Holland Akan Aikin Gona

FB IMG 1716382382652

Gwamna Yusuf Ya Yi Haɗin gwiwa da Gwamnatin Ƙasar Netherland domin Tsaron Abinci, Sauyin Yanayi

Alfijir labarai ta ruwaito Gwamnai Abba Kabir Yusuf ya nemi kasar Netherland ta ba da goyon bayan diflomasiyya domin habaka noma da rage tasirin sauyin yanayi a jihar.

Gwamnan ya bayyana shirin kulla huldar diflomasiyya da gwamnatin kasar Holland, a lokacin da ya karbi bakuncin Ms Eva De Wit, Sakatariyar a Ofishin Jakadancin Netherland a Najeriya.

Yusuf ya jaddada tasirin da Holland dake dashi a kan noma da sauyin yanayi a Turai.

Yayin da yake sanar da tawagar kasar Holland matakin da ya dauka game da alkaluman shan muggan kwayoyi da suka gada daga gwamnatin da ta shude, Gwamna Yusuf ya ce an bude cibiyoyin koyar da sana’o’i 24 domin samun kwarin guiwar matasa, su dogara da kansu.

Yusuf ya kara da cewa gwamnatin sa ta kuma gyara halayen wasu matasa kusan 713 da suka tsunduma kansu cikin ayyukan ‘yan daba ta hanyar hadin gwiwa da ‘yan sandan Najeriya domin dakile tashe-tashen hankula a jihar.

A nata bangaren, Ms De Wit wadda ita ma ta samu rakiyar Shugaban Ofishin Jakadancin, Hukumar Kula da ‘yan gudun Hijira ta Duniya, Mista Laurent De Boeck, ta yi alkawarin hada kai da gwamnatin jihar Kano a fannonin inganta rayuwar matasa, samar da abinci da kuma sauyin yanayi.

FB IMG 1716382399443
📸 Sabature
FB IMG 1716382388285
📸Sabature

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *