Shugaban Jami’ar Mata Zalla Tazkiyah, da ke Zaria Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya ba wa mata marayu gurbin karatu a Jami’ar.
Jami’ar Tazkiyah Zaria ita ce ta farko a Nijeriya wadda mata ne kawai za su yi karatu a cikinta. An zabo wadanda suka cancanta daga sassa daban-daban na Nijeriya.
An bayar da wannan gurbin karatun ne ba tare da la’akari da kabila ko addinin wadda ya samu ba.
Farfesa Ibrahim Garba Satatima, tsohon Shugaban Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci na Jami’ar Bayero, Kano ya yaba wa wannan hidima ga al’umma inda ya kwatanta ta da irin wadda marigayi Gani Fawehinmi ya ba wa matasan Nijeriya a matsayin abin yabawa.
Malamin ya kuma addu’ar fatar samun nasara ga wannan Jami’ar .
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t