Labari Mai Dadi: Kamfanin Dangote ya rage farashin litar man fetur.

Matatar Dangote

Daga Aminu Bala Madobi

Kamfanin Dangote ya sanar da rage farashin tacaccen man fetur din da yake sayarwa a kamfanonin sa ga dillalan man a Najeriya.

Mai magana da yawun kamfanin Anthony Chiejina yace sun rage farashin ne daga naira 990 kowacce lita zuwa naira 970 domin saukakawa jama’ar Najeriya.

Sanarwar ta ce kamfanin na Dangote ya dauki wannan matakin ne domin nuna godiya ga ‘yan Nijeriya bisa goyon bayan da suke ba Dangote.

Idan dai za a iya tunawa kamfanin Ɗangote ya Fara sayar da man matatarsa ne akan farashin Naira 990 ga dillalai, sai dai ya sha fama da kalubale daga bangarori daban-dabam.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *