Labari Mai Dadi! Tinubu Ya Bada Umarnin Gaggawa Akan Bunkasa  Matatar Ɗangote

IMG 20231218 003430

Majalisar zartaswa ta tarayyar Nigeria ta umurci kamfanin man fetur na kasa (NNPC) da ya sayar da danyen mai ga matatar Dangote da sauran matatun cikin gida da kudin kasar nan naira ba dalar Amurka ba.

Alfijir labarai ta ruwaito shugaban hukumar tattara kudaden haraji ta tarayya (FIRS) Zack Adedeji ya bayyana haka bayan taron FEC da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Litinin.

Adedeji ya ce matakin zai rage radadin kudaden da kasar ke kashewa a kasashen waje tare da daidaita farashin man fetur da dizal da sauran kayayyakin da ake amfani da su a Najeriya.

Ya kara da cewar majalisar zartarwar ta ba da umarnin cewa ba tare da bata lokaci ba hukumar NNPCPL ta fara aiwatar da wannan umarni don bunkasa masana’antun man fetir na gida Najeriya.

Shugaban hukumar tattara kudaden shigar ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta bayar da umarnin matatar Ɗangote ita ma ta sayar da tataccen man ga yan kasuwar mai na gida da naira ba dalar Amurka ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *