Labari Mai Dadi! Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – In Ji Mr. Robert

Screenshot 20240429 110425 Facebook

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya samu masu zuba jarin dala miliyan 600 daga kamfanin sufurin jiragen ruwa na kasar Denmark, AP Moller-Maersk, domin fadada ayyukan tashar jiragen ruwa da ake da su da karin ayyukan jigilar kaya a tashoshin jiragen ruwa na Najeriya.

Alfijir Labarai ta ruwaito Shugaban Kamfanin A.P Moller-Maersk, Mista Robert Maersk Uggla ne ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da Shugaba Tinubu a gefen taron tattalin arzikin duniya na musamman kan hadin gwiwa, ci gaba da makamashi a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa zuba jarin zai taimaka wajen sake gina tashoshin jiragen ruwa a sassan gabashi da yammacin Najeriya.

Shugaban ya ce, hakan zai kara tallafawa kokarin sabunta tashoshin jiragen ruwa na kasar nan, da nufin inganta harkokin kasuwanci, da saukaka shigo da kayayyaki, da rage cin hanci da rashawa a tashoshin jiragen ruwa, tare da inganta harkokin kasuwanci.

Shugaban ya tabbatar wa Maersk kudirin gwamnatinsa na hada kai da samar da yanayin da zai sa ‘yan kasuwa su bunkasa a kasar.

Ya ba da misali da hadin gwiwar da Maersk ta yi a baya wajen bunkasa tashar ajiye sundukai ko kwantainoni a Jihar Ogun a matsayin wata shaida ta hadin gwiwa mai inganci tare da kamfanin hada-hadar kayayyaki.

Da yake karin haske game da dadewar da kamfanin Maersk ke yi a Najeriya da kuma yadda ya yi imani da makomarsa, Shugaban Kamfanin A.P Moller-Maersk, Mista Robert Maersk Uggla ya ce kamfaninsa ya zuba jarin sama da dala miliyan dubu 2 a tashoshin jiragen ruwa na Najeriya da sauran ayyuka.

Ya kuma jaddada yiwuwar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya za su iya daukar manyan manyan jiragen ruwa, sannan ya jaddada bukatar fadada ayyukan tashar jiragen ruwa domin biyan bukata, tare da rage tsadar kayayyaki.

“Mun yi imani da Najeriya, kuma za mu zuba jarin dala miliyan 600 a kayayyakin nan da kuma sanya tashoshin jiragen ruwa su zama masu daukar manyan jiragen ruwa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *