Lauyoyin hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum sun buƙaci kotun Ecowas da ta umurci a mayar da shi kan mulki kasancewar hamɓarar da shi da aka yi da kuma tsare shi sun saɓa wa doka.
Alfijir Labarai ta rawaito an tsare da Bazoum ne tun bayan da sojoji masu gadin fadar shugaban ƙasar suka hamɓarar da shi daga mulki ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Sojojin sun zargi gwamnatin Bazoum da gaza magance matsalar tsaron ƙasar.
Sai dai É—aya daga cikin lauyoyinsa waÉ—anda suka garzaya kotun Ecowas, Seydou Diagne, a bayanin da ya yi, ya buÆ™aci kotun, wadda ke zaman ta a Najeriya ta yanke hukunci cewar “hamÉ“arar da shi da aka yi Æ™arfi da yaji take hakkinsa ne na shiga harkokin siyasa.”
Kotun Ecowas, kotu ce wadda kan yanke hukunci kan ƙararraki daga ƙasashen yammacin nahiyar Afirka, sai dai ba wajibi ne ga ƙasashe su yi amfani da hukuncin kotun ba kasancewar babu takamaiman tsarin tabbatar da hukuncin.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp