Likitoci sun janye yajin aiki, sun kuma gindaya sabon sharaɗi

FB IMG 1764520014260

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar.

Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni huɗu, domin bai wa gwamnatin Tarayya damar aiwatar da muhimman buƙatun da suka gabatar.

Ya ce an cimma matsayar ne bayan saka hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ta ƙunshi ci gaban da aka samu kan manyan buƙatu 19 na ƙungiyar, ciki har da biyan bashin albashi da alawus-alawus da sauran haƙƙoƙinsu.

Suleiman ya ce Majalisar Koli ta dakatar da yajin aikin ne a matsayin wata alama ta kyakkyawan fata, domin a ci gaba da sa ido kan yadda gwamnati za ta aiwatar da alƙawuran.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta yi amfani da wannan wa’adi na makonni huɗu domin ƙara faɗakar da ’yan Najeriya da kuma ci gaba da tattaunawa da gwamnati.

Yajin aikin ƙungiyar ya bar asibitoci 91 cikin mawuyacin hali, kasancewar likitoci 11,500 — waɗanda su ne manyan ginshiƙai da ke kula da marasa lafiya a ƙasar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *