Gwamnatin Kano ta bayyana matsayarta kan dawowar Achaba a fadin jihar

FB IMG 1764563775662

Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana daukar matakan gaggawa don dakile dawowar masu baburan haya (Achaba) da ake gani a sassa daban-daban na birnin Kano duk da haramcin da aka dade da yi na Achaba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Ibrahim Waiya ya sanyawa hannu a ranar Lahadi.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ta ce rahotannin sirri sun tabbatar da karuwar aikace-aikacen Achaba har a wasu yankunan iyaka, tare da gano wasu da ba a san ko su wanene ba da ke shiga al’ummomi suna aiki da babura a matsayin haya.

Gwamnatin ta ce hukumomin tsaro suna kan lamarin, kuma gwamnati za ta kara musu goyon baya don tabbatar da tsaro a duk kananan hukumomi 44.

Ta ce tana nazarin shawarwarin jama’a kan kara tsaro, musamman a hanyoyin shiga da fita na jihar.

Hakazalika ta jinjinawa jama’a bisa kulawa da bayar da rahotanni, tare da tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf yana aiki tare da manyan shugabanni da hukumomin tsaro domin tabbatar da kwanciyar hankali a Kano.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *