Ma’aikatan CBN 1,500 za su fara aiki bayan maida wani sashen bankin zuwa Legas

IMG 20240111 105954


Akalla ma’aikatan babban bankin Najeriya, CBN, 1,500 ne za su koma aiki a ofishin bankin na Legas a ranar Juma’a mai zuwa, bayan canjin wajen aiki da aka yi musu daga hedikwatar.

Alfijir labarai ta rawaito wata majiya a babban bankin ta shaida wa wakilin PUNCH din cewa shirin, duk da cewa ya na shan suka daga ƴan Nijeriya, har yanzu yana nan daram kuma ma’aikatan za su fara aiki ranar Juma’a.

“Eh, har yanzu shirin yana kan aiki kuma za su fara aiki a ranar 2 ga Fabrairu, wanda shine makon farko na wata mai zuwa,” in ji wani jami’in.

Wannan sabon mataki na zuwa ne biyo bayan matakin da sabon shugaban bankin ya dauka na mayar da wasu sassan ma’aikatun CBN zuwa cibiyar tattalin arzikin kasar domin kare lafiyar ma’aikata, da bunƙasa aiki da kuma rage cunkoso a babban ofishinsa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *