Wata Sabuwar! Ana Shirin Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC

📸Umar Abdullahi Ganduje

Alamomi masu karfi sun bayyana kan yunkurin tsige Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, daga kujerarsa.

Alfijir labarai ta rawaito majiyoyi sun ce wasu masu ruwa da tsakin APC daga yankin Arewa ta Tsakiya da na hannun damansu ne suke kokarin raba Ganduje da kujerar domin ta koma yankin.

Wasu rahotanni sun bayyana yadda tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, yake neman goyon bayan masu ruwa da tsaki domin darewa kan kujerar shugaban jam’iyyar APC.

Hotunan Yahaya Bello na neman shugabancin APC dai sun karade Abuja, awa 48 da saukarsa daga kujerar gwamna, kuma a daidai lokacin da jami’yyar ke shirin gudanar da babban taronta na kasa.

A watan Agustan 2023 ne Ganduje, tsohon Gwamnan Kano, ya zama shugaban APC na kasa bayan magabacinsa Sanata Abdullahi Adamu, ya yi murabu.

Abdullahi Adamu ya yi murabu ne sakamakon rikicin cikin gidan jam’iyyar, wanda wasu ke zargin yana da alaka da rashin goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2023.

Zaman Ganduje shugaban APC abi yi wa masu ruwa da tsakin Arewa ta Tsakiya dadi ba, kasancewar daga yankin Abdullahi Adamu ya fito, don haka suke ganin daga nan ya makata a samu wanda zai karashe wa’adinsa.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka, kan wannan dambarwa, amma wayarsa ba ta shiga.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

One Reply to “Wata Sabuwar! Ana Shirin Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *