Maganar Gaskiya! Babu hannun mu a tashin farashin kayan abinci — Alh Aliko Dangote

FB IMG 1708719561389

Babbar Darakta a rukunin kamfanonin Dangote, Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta bayyana cewa rukunin kamfanonin Dangote ba su da hannu a tashin farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a kasar nan.

A wata hira da Sashen Hausa na BBC, Hajiya Fatima ta ce kamfanin ya sayar da bangaren sarrafa abinci shekaru biyar da suka gabata ga Olam Group da ke sarrafa abinci da kasuwancin noma a Najeriya.

Ta ce Olam a yanzu shi ne ke samar da fulawa, taliya, semolina, kuma duk wata fulawa da ake samu a kasuwanni ba kamfanin Dangote ne ke samar da ita ba.

“A cikin yarjejeniyar cinikin, an amince da cewa za su ci gaba da yin amfani da sunanmu da tambarin muwajen yin kayayyakinsu, kuma nan da shekara mai zuwa za su daina.

“Mu yanzu sukari, gishiri, da kayan yaji na Dangote kawai muke samarwa. Har ila yau, muna fatan za mu fara noman shinkafa nan gaba ko kuma badi,” in ji ta.

Fatima ta kara da cewa ba su ji dadin yadda farashin kayayyakin ke hawa ba kuma kamfanin ba zai iya maganin hakan ba, inda ta nuna fatan abubuwa za su daidaita nan ba da jimawa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *