…Sheleru ya amince cewa kwayoyin da aka kama nasa ne, haka kuma gidan da aka gano su nasa ne.
Alfijir labarai ta rawaito an cafke wani tsohon kansila da ya yi wa’adin mulki biyu a karamar hukumar Ibeju-Lekki ta jihar Legas, Sheleru Sadiq Olalekan, bayan jami’an Hukumar Yaki da Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun gano yana da hannu wajen sayarwa da safarar miyagun kwayoyi.
A wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, ya ce an kama tsohon kansilan mai shekaru 45 a ranar Litinin 2 ga Maris, 2026 a gidansa da ke Ilado a Ibeju-Lekki. Bayan bincike da aka yi a gidan, jami’an sun gano kilo 40 na tabar wiwi nau’in skunk a cikin daya daga cikin dakunan gidan.
A bayanin da ya bayar, Sheleru ya amince cewa kwayoyin da aka kama nasa ne, haka kuma gidan da aka gano su nasa ne. Ya kuma bayyana cewa ya taba zama kansila sau biyu yana wakiltar al’ummar Orimedu a karamar hukumar Ibeju-Lekki.
A birnin Abuja kuma, jami’an NDLEA sun kama wani dan kasuwa mai shekaru 32 mai suna Emeka Hyginus Okwor a ranar Talata 3 ga Maris. An kama shi ne a cikin mota da ta taso daga Obollo-Afor a jihar Enugu zuwa Zuba a babban birnin tarayya, inda aka gano kwayoyi 1,000 na tapentadol 250mg boye a cikin pampers na jarirai a cikin kayansa.
Wanda ake zargin ya amsa cewa kwayoyin nasa ne, kuma ya bayyana cewa yana kai su kauyen Guduwa da ke karamar hukumar Gurara a jihar Neja, inda yake da wani shagon kayan masarufi.
Hakanan kuma, jami’an NDLEA sun tare wata mota a kan hanyar Kabba zuwa Obajana a jihar Kogi, inda suka gano kilo 1.55 na tabar wiwi ta roba nau’in Colorado boye a cikin kwalin fan. An kama wani dan kasar Kamaru mai shekaru 36 mai suna Mey Ali Muhamat, wanda ke kan hanyarsa daga Legas zuwa Kamaru ta Lokoja, Kano da Maiduguri.
A jihar Neja kuwa, jami’an sintiri sun tare wata motar bas da ta taso daga Ibadan a ranar Laraba 4 ga Maris, inda suka gano sassan na’urorin fashewa na IED guda 500 boye a cikin buhu. Binciken da aka biyo baya ya kai ga kama wanda ake zargi zai karbi kayan, Osama Abdullahi mai shekaru 21 a garin Pelegi da ke karamar hukumar Mashegu.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t