Majalisar Jihar Kano Ta Bankado Badakalar Kudi A Wasu Hukumomin Gwamnati

๐Ÿ“ธ Kano House

Daga Aminu Bala Madobi

Majalisar dokokin jihar Kano ta bankado badakalar kudi a hukumar Karota da wasu hukumomin gwamnatin jihar.

Alfijir labarai ta rawaito Majalisar ta bukaci hukumar Karota ta mayar da fiye da naira miliyan 257 zuwa asusun gwamnatin Kano.

Cikin hukumomin da aka nemi su mayar da kudin sun hada da hukumar lafiya a matakin farko da zata mayar da fiye da naira miliyan 2 sai hukumar dabโ€™I da zata mayar da fiye da naira miliyan 1.

Wannan ya biyo bayan rahoton kwamitin kula da kashe kudaden gwamnati da kwamitin ya gabatar na shekarar 2021 a zaman majalisar ranar Litinin

Cikin shawarwarin da kwamitin ya gabatar karkashin shugaban sa Tukur Muhammad Fagge, ya bukaci hukumomin da su mayar da wadannan kudade da suka yi batan dabo.

Haka zalika majalisar zata dauki hukunci kan wadanda ake zargi da rashin tafiyar da kudin yadda ya kamata.

Da yake jawabi ga manema labarai shugaban kwamitin kula da yadda ake kashe kudaden gwamnati dan majalisa mai wakiltar Fagge, Tukur Muhammad, ya ce wannan na cikin rahoton da mai binciken kudi na jiha ya gabatarwa majalisa.

Nasara Radio ta rawaito cewa, Dan majalisar yace duk lokacin da mai binciken kudi ya gama aikin sa yana mikawa majalisa, kuma majalisa tana gayyatar duk maโ€™aikatar da aka samu da zargin rashin tafiyar da kudi yadda ya dace.

Ya ce idan kwamiti ya kira hukuma ko maโ€™aikata ta kare kanta ta gaza yin haka to ba abinda ya ragewa kwamiti saidai ya bada shawarar dawo da wadannan kudi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *