Majalisar dokokin jihar kano ta tantance tare da amincewa gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya nada karin mutane ukun da ya tura mata suna don tantance su domin nada su a matsayin kwamishinoni.
Alfijir Labarai ta rawaito mutanen da majalisar ta tantance sun hadar da Hon. Amina Abdullahi Sani daga karamar hukumar Nasarawa, Ali Namadi daga karamar hukumar Dala sai kuma Hon. Ibrahim Jibril Daga karamar hukumar Fagge.
Shugaban majalisar Hon. Isma’il Jibril Falgore ne ya bayyana hakan ga menema Labarai Jim kadan bayan aikin tantance su a zauren majalisar.
Hakan na kunshe ne cikin wata takarar da gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya aikewa majalisar a ranar Alhamis , wadda Shugaban majalisar ya karanta a gaban majalisar domin amincewa .
A zamanta na yammacin wannan rana bayan tambayoyi da tattaunawa, majalisar ta amincewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada wadanda ya tura mata sunayen su.
Majalisar ta kuma tantance tare da amincewa da nadi Justice Dije Aboki a matsayin alkalin alkalai ta jihar kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ