Malumfashi Ya Godewa Gwamna Yusuf Bisa Sake Nada shi Shugaban KANSIEC.

IMG 20241208 WA0621

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya bayyana godiyar sa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya sake nada shi a matsayin shugaban hukumar.

Farfesa Malumfashi ya bayyana haka ne a yayin bikin bayar da lambar yabo da jami’an hukumar da ma’aikatan hukumar suka shirya domin girmama salon shugabancin sa a zaben kananan hukumomi na 2024 da ya gabata.

Malumfashi ya ci gaba da cewa matakin da Gwamna Yusuf ya dauka na sake nada shi shaida ce dake nuna amana, halin jarumta da kuma kwarin gwiwar da aka yi masa.

Farfesa ya danganta nasarar zaben ga Allah Madaukakin Sarki, yayin da ya ce duk wani kura-kurai da aka samu ba da gangan ba ne, ya kuma nemi gafara daga wadanda basu ji dadi ba.

Daganan Malumfashi ya kuma godewa mambobin hukumar da dukkan ma’aikatan hukumar bisa goyon baya da hadin kai da suka ba shi a lokacin gudanar da zaben.

Kwamishinan tsaro da bayanan sirri, Alhaji Shehu Muhammad Na’Allah Kura ne ya bayar da lambar yabon ga Farfesa Malumfashi, in da ya yaba da salon shugabancin sa da kuma yadda yake sauraron mutane a ko da yaushe.

Kura ya lura cewa Farfesan mutum ne mai sanyin hali wanda kan iya sake la’akari da shawarar da ya yanke idan aka gabatar ma sa da hujjoji masu ma’ana.

Ya ƙara da cewa, bisa wannan dalilai, mambobin hukumar da ma’aikatan suka karrama shi da babbar lambar yabo a madadinsu, don nuna godiya bisa ga yin aiki karkashin jagorancin sa abin kwatance.

A cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na hukumar Bashir Habib Yahya ya sanya wa hannu, ya ce an bayar da lambar yabon ne a madadin mambobin hukumar da ma’aikatan hukumar domin nuna jin dadin shugabancin Farfesa Malumfashi.

Aminu Bala Madobi, Media Aide, KANSIEC Chair

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *