Mataimakin shugaban Najeriya Ya Jaddada Bukatar Karfafa Alaka Tsakanin Najeriya Da Kungiyar Tarayya Turai

FB IMG 1724967787315

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jaddada bukatar karfafa alaka tsakanin Najeriya da kungiyar tarayyar turai, musamman wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki da sauran kalubalen jin kai da kasar ke fuskanta.

Alfijir Labarai ta rawaito ya bayyana jin dadin Najeriya da irin tallafin da kungiyar EU ke baiwa kasar, ya kuma bayyana muhimmancin ci gaba da yin hadin Gwiwa a tsakanin ƙasashen biyu.

Yayin wata ziyarar ban girma da tawagar EU Ƙarƙashin jagorancin Jakadiyar Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS mai barin gado, Samuela Isopi, a ranar Alhamis din da ta gabata a fadar shugaban kasa da ke Abuja, mataimakin shugaban kasar ya mika matukar godiya ga irin gudunmawar da Ambasada Isopi ta bayar a lokacin da take rike da mukamin.

Mataimakin shugaban kasa Shettima ya bayyana cewa, “Kun taka rawar gani sosai wajen inganta alaka tsakanin EU da Najeriya. Taimakon da ku ke yi a ayyukan jin kai a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, da kuma inganta kasuwanci tsakanin kasashenmu, ya taka rawar gani sosai.”

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *