Matar ɗan Majalisar Wakilai daga jihar Bauchi ta ba da mamaki a yayin da ta raba damin rake ga al’ummar mazabar mijinta a matsayin wani ɓangare na shirin “Dogaro da Kai”.
Wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce sosai, inda jama’a da dama suka bayyana mamaki kan yadda mace mai matsayi a siyasa za ta fito da irin wannan tallafi a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa.
A cewar ta, wannan rabon na nufin karfafa wa mata da matasa gwiwa su ci gaba da gudanar da sana’o’in gargajiya.
Duk da haka, ayayin da Ake sa ran wakilai da iyalansu su rika kawo hanyoyin cigaba da na zamani, ba wai rabon kayan gargajiya kamar rake ba. Wasu sun bayyana damuwa cewa wannan al’amari ya nuna yadda ake cin fuskar talaka da sunan ana tallafa masa
A duk inda ka juya a Najeriya, ka kan gamu da abubuwan mamaki da shugabanni ke aiwatarwa amatsayin ayyukan azo a gani ga Jama’ar su saidai kuma hakan fallasa cin fuska ne ga talakawa.
‘Yan majalisa suna karɓar makudan kudade domin ayyukan mazabu (alhali ma cewa akwai shakku ko wannan doka ce), amma sai su bige raba rigunan sanyi kamar wani Shugaban Karamar Hukuma yayi a Jihar Jigawa, wanda a wannan lokaci uwargidan Dan Majalisar Tarayya Daga Bauchi ta sayi rake ta rabawa talakawa a matsayi ayyukan mazabu.
Ta yaya za a ce mutum yana karɓar sama da Naira miliyan 35 a wata a matsayin albashi da alawus, kuma yana da kusan biliyan daya na kudin aikin mazabu, amma abin da zai raba wa jama’a “a matsayin taimako” shi ne rake? Wannan cin zarafi ne sosai.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t