Daga Aminu Bala Madobi
Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo sun bankado wata mummunar aika aikta da ta daɗe ana zargin wasu bata-garin da yi a boye.
Rahotonni sunce cikin wani hotel da ake tunanin ana zama ne kawai a ciki, aka gano an mayar da shi cibiyar tsafi, inda ake kai mutane ana yanka su, acire wasu sassa domin yin mugayen ayyuka.
Wannan samame da rundunar ta jagoranta ya girgiza tunanin al’umma, musamman ganin yadda ake ga zunzurutun mutane a yayyanke domin gudanar da tsafe tsafe .
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, CP Danjuma Aboki, shi ne ya jagoranci wannan gagarumin samame bayan samun sahihan bayanai daga wasu masu kishin ƙasa. A lokacin da jami’an suka kutsa kai cikin hotel ɗin, sai suka tarar da gawarwaki da dama, wasu an cire musu sassan jikinsu. Wannan al’amari ya tabbatar da irin barnar da wasu bata-garin ke aikatawa a boye, da rashin darajar rayuwar ɗan Adam.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana mamaki da firgici, inda suka roƙi hukumomi da su ƙara tsaurara matakai domin kare rayuka da dukiyoyi. Wannan mummunan lamari ya nuna bukatar mutane su rika bada muhimmanci wajan kulawa da juna da wayar da kan jama’a.
Allah ya kare mu daga sharrin mutane marasa imani da sharrin aljannu, ya tabbatar mana da zaman lafiya da tsaro a ƙasar nan


Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t