Me Ya Kamata Jiharku Tayi da Bashin Gwamnatin Tarayyar?

A matsayin ka/ki na dan kasa, me ka ke ganin ya dace jiharka/ki ta yi da nata 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da bai wa jihohin ƙasar 36 tallafin naira biliyan 656.112.

Bayanan tallafin sun fito ne yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ranar Alhamis.

Wata sanarwa daga ofishin Mista Osinbajo ta ce kowace jiha za ta samu naira biliyan 18.225, wanda za ta biya cikin shekara 30 kan kuɗin ruwa kashi 9 cikin 100.

A cewar fadar shugaban ƙasa, an ɗauki matakin ne saboda a tallafa wa jihohi cimma muradansu na harkokin kuɗi musamman kasafin kuɗaɗensu na shekara.

Za a raba kuɗin ne a mataki shida cikin wata shida kuma ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN) za a rarraba wa jihohin.

BBC sun tawaito Cewar Tun a watan Yuli ne Ministar Kuɗi Zainab Ahmad ta faɗa wa majalisar cewa za a fara zarar kuɗi daga asusun jihohin domin fara biyan bashin tallafin farko da aka ba su, amma sai jihohin suka nuna turjiya tare da neman wani agajin, abin da ya sa aka ɓullo da agajin kasafin kuɗin kenan.

Wannan bashin makudan kudade, da gwamnatin tarayyar Najeriya za ta bawa jihohin kasar nan! 

A matsayin ka/ki na dan kasa, me ka ke ganin ya dace jiharka/ki ta yi da nata kudin?

One Reply to “Me Ya Kamata Jiharku Tayi da Bashin Gwamnatin Tarayyar?”

Comments are closed.