Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi murabus daga mukaminsa domin neman tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi.
An bayyana hakan ne a ranar Litinin cikin wata takaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar.
Ya ce, “An tabbatar da murabus din mai girma Ministan Harkokin Waje.”
Rahotanni sun nuna cewa Tuggar na daga cikin ministoci hudu a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ake sa ran za su sauka daga mukamansu domin yin takara.
Tun da farko, mai ba ministan shawara kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Alkasim Abdulkadir, ya tabbatar da cewa Tuggar na da sha’awar tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi.
A cewarsa, “Ministan yana da burin tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi.”
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t