Ministan Lantarki Ya Yi Barazanar Ƙwace Lasisin Kamfanonin Rarraba Wuta A Najeriya

FB IMG 1709764262739

Ministan Lantarki na Nijeriya Bayo Adelabu ya yi barazanar ƙwace lasisin kamfanonin rarraba wuta na ƙasar Discos, yana mai cewa ba za a lamunci yanayin da suke saka mutane na ƙarancin wutar ba a faɗin ƙasar.

Alfijir labarai ta rawaito ministan, wanda ya wallafa saƙon barazanar a shafinsa na X a ranar Laraba, ya ce ya damu matuƙa da taɓarɓarewar samar da wuta da ake fama da rashin ta a faɗin ƙasar.

“A don haka ne ma na kira shugabannin Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC) da na Ibadan (IBEDC), da kuma shugaban Kamfanin Samar da Lantarki na Nijeriya TCN don yin wata ganawa mai muhimmanci,” in ji Ministan.

Ya ce ya kira taron ne don tattaunawa kan yadda ake matuƙar fama da matsalar samun wuta a waɗannan yankunan da kuma nemo mafita ta dindindin.

As the Minister of Power, I am deeply concerned about the deteriorating electricity supply across the country. In response to this pressing issue, I have summoned the Chief Executives of Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) and Ibadan Electricity Distribution Company…

— Bayo Adelabu (@BayoAdelabu) March 6, 2024


Rahotanni sun ce ana matuƙar fama da ƙarancin wuta a wasu sassan Nijeriya musamman babban birnin ƙasar Abuja, a daidai lokacin da yanayin zafi ke kunno kai.

“Abin takaici ne ganin yadda ake samun raguwar wutar lantarki duk da ƙoƙarin da ake yi na inganta lamarin. Ma’aikatar Lantarki ta matsa lamba kan Kamfanonin da ke Samar da Wutar (GENCOs) don inganta ayyukansu, lamarin da ya sa aka samu ƙaruwar samar da wuta zuwa sama da megawat 4000,” a cewar Ministan.

Sai dai Mista Adelabu ya bayyana cewa duk da wannan ci gaba da ake samu, wasu kamfanonin sun gaza rarraba wutar da TCN ke bayarwa yadda ya kamata.

Ya kuma koka kan yadda yawan ɓarnata kayayyakin samar da wutar da ake yi ke kara ta’azzara matsalar a yankuna kamar Abuja da Benin da Fatakwal da kuma Ibadan.

Minista Adelabu ya sha alwashin cewa daga yanzu zai kama dukkan kamfanonin rarraba wutar da alhaki idan har ba su yi abin da ya kamata ba.

“Ba za a lamunci rashin yin aiki yadda ya dace da gangan ba, kuma ana iya ɗaukar matakai masu tsauri ciki har ƙwace lasisi. Bugu da ƙari, na umurci TCN da ta ba da fifiko ga ayyukan gyare-gyare na tasoshin da layukan wutar lantarki da suka lalace don inganta samar da wuta a yankunan da abin ya shafa.”

TRT Afrika

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *