Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta fitar da sanarwar neman afuwa bayan daya daga cikin motocin ceton al’umma tayi karo da wata mota mallakar wani mutum, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane uku da raunata daya.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Kwamandan hukumar a babban birnin tarayya Abuja, Momodu Ganiyu, ya bayyana cewa hukumar na cikin matukar bakin ciki da nadama game da wannan mummunan lamari.
Lamarin ya faru da yammacin ranar Juma’a a kusa da junction na ECOWAS da ke Wuse 2, Abuja, yayin da ake aikin kashe gobara a wani wuri mai suna Avenue Plaza, Banex.
Ya ce motar na tafiya da sauri tare da karar kararrawar, ta ci karo da wata mota kirar Toyota Camry da ke fitowa daga wata hanya a junction ɗin.
Daily Nigerian
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD