Motar ƴan kwana-kwana ta hallaka matasa uku a hadarin mota a Abuja

FB IMG 1746970742852

Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta fitar da sanarwar neman afuwa bayan daya daga cikin motocin ceton al’umma tayi karo da wata mota mallakar wani mutum, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane uku da raunata daya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Kwamandan hukumar a babban birnin tarayya Abuja, Momodu Ganiyu, ya bayyana cewa hukumar na cikin matukar bakin ciki da nadama game da wannan mummunan lamari.

Lamarin ya faru da yammacin ranar Juma’a a kusa da junction na ECOWAS da ke Wuse 2, Abuja, yayin da ake aikin kashe gobara a  wani wuri mai suna Avenue Plaza, Banex.

Ya ce motar na tafiya da sauri tare da karar kararrawar, ta ci karo da wata mota kirar Toyota Camry da ke fitowa daga wata hanya a junction ɗin.

Daily Nigerian

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *