Mun Ceto Mutum 6 Da Dukiyar Miliyan 107 A Kano – In Ji Hukumar Kashe Gobara

IMG 20240206 WA0144

Hukumar ta ja hankalin mutane kan kula da ababen amfani na gida.

Alfijir labarai ta rawaito hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta sanar da ceto rayukan mutum shida da dukiyar Naira miliyan 107 daga gobara 74 da suka faru a watan Fabrairun 2024, a jihar.

Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ne, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Juma’a a Kano.

Abdullahi, ya kuma ce mutum hudu ne suka rasa rayukansu, yayin da gobarar ta kone dukiyar Naira miliyan 64.

“Mun samu kiran kai agaji bakwai daga kiran waya 10 daga mazauna jihar,” in ji shi.

Ya shawarci jama’a da suke kula sosai da abin da ya shafi wuta da lantarki.

Kazalika, ya ce wasu daga cikin gobarar sun tashi ne sanadin gas din girki.

Har wa yau, ya ce akwai bukatar mutanen jihar suke neman bayanai game da abin da ya shafi gobara da hanyoyin kare ta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *