Wata Sabuwa! Gwamna Ya Tube Rawanin Hakimai Guda 2

ALFIJIR 1

Gwamnatin ta kama hakiman biyu da laifin rashin yi mata biyayya.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tube rawanin Hakimin Sauwa, Alhaji Muhammad Tajudden-Sauwa, bisa laifin rashin yi mata biyayya. Kazalika, gwamnatin ta dakatar da Hakimin Guluma na tsawon wata shida, Alhaji Muhammad Bashir-Guluma.

Alfijir labarai ta rawaito babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Kebbi, Alhaji Ahmed Idris ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, a ranar Asabar.

Idris, ya ce kwamitin da hukumar kula da ma’aikata ta Karamar Hukumar, ta kafa a ranar 31 ga watan Janairu, ta samu masu sarautun gargajiyar biyu da laifin rashin yin biyayya ga gwamnatin jihar.

An kafa kwamitin ne biyo bayan korarin da shugaban Karamar Hukumar Arugungu ya kai na hakiman biyu.

Ya ce kwamitin ya bayar da shawarar mataki karkashin dokar ma’aikatan gwamnati mai lamba 030301(0), wadda ta shafi rashin yin biyayya.

Idris, ya ce hukuncin dakatar da hakiman biyu za ta fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Fabrairu, 2024.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *