Murja Kunya ta Maka Hukumar Hisba Da Kwamishinan Yan Sandan Kano A Gaban Kuliya

FB IMG 1708265600330

Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Nasiru Saminu ta umurci hukumar Hisbah ta jihar Kano da hukumar kula da asibitocin jihar Kano da su ba da damar lauyoyin Murja Ibrahim Kunya su ganta.

Alfijir labarai ta rawaito wadanda akai karar sun hada da kwamishinan Shari’a jihar Kano, alƙalin kotun Shari’ar Musulunci dake Kwana hudu Malam Nura Yusuf Ahmed, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, hukumar kula da asibitocin jihar Kano, asibitin masu tabin hankali na tarayya dake Dawanau.

Murja a cikin wata takarda da lauyanta ya gabatar, ta roki kotu da ta umarci wadanda ake kara na 4 da na 5 da su ba ta dama a rika ganin Murja, matukar bukatar hakan ta taso ba tare da wata matsala ba.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Mai shari’a Nasiru Saminu ya amince da bukatar Murja Kunya da lauyanta.

Kotun ta kuma umurci wanda ake kara na 5 Hukumar Kula da Asibitin Jihar Kano da ta bai wa mai lauyan Murja kunya kwafin rahoton lafiyar kwakwalwar da aka yi mata.

Babbar kotun ta kuma umurci wanda ake kara na 2 alƙalin kotun Shari’ar Musulunci dake kwana hudu da ya dakatar da ci gaba da gudanar da shari’ar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci Shari’ar dake gaban babbar kotun sannan ta bayar da kwafin gaskiya na shari’ar ga lauyan wanda ya shigar da kara.

Hakazalika kotun ta kuma dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 20/03/2024.

Kotun Shari’ar Musulunci dake Samantha a Kano unguwar kwana hudu a zaman ta na karshe, ta bada umarnin kai Murja kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiya ƙwaƙwalwarta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *