Mutane 17 sun bace yayin da kwale-kwalen ke dauke da mutane 23 ya kife a Adamawa

Har yanzu ba a tantance mutane 17 ba bayan da jirgin ruwan dauke da mutane 23 ya kife a jihar Adamawa.

Alfijir Labarai ta rawaito Wani kwale-kwalen da ke jigilar mutanen yankin ya kife a tafkin Njuwa da ke kan kauyen Rugange a karamar hukumar Yola ta Kudu

A cewar wani ganau, Faisal Dabo Rugange, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a a lokacin da wadanda abin ya shafa za su je garin Yola domin harkokin kasuwanci.

“An yi ruwan sama a lokacin da hatsarin ya afku.

Wata Gagarumar guguwa ce ta kada ruwa a cikin kwale-kwalen kuma nan take ya kife,” inji Faisal.

Ya kara da cewa, duk da cewa jirgin ruwan na dauke da fasinjoji sama da 20, wasu maaumta ne suka kubutar da su shida kawai daga cikinsu.

Faisal wanda ya koka da yadda al’ummar Rugange ke fama da tashe-tashen hankula sakamakon ambaliya da ruwa mai yawa a kogin Binuwai, ya ce mutanen na bukatar manyan kwale-kwalen zamani a yankin.

Sakataren zartarwa na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, Mohamed Suleiman, ya ce mutum daya ya mutu, an ceto biyar sannan ba a ga wasu 17 ba.

Shi ma da yake magana kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya ce rundunar ta tura jami’an ‘yan sandan ruwa domin su taimaka a aikin ceto.

Ya kara da cewa har yanzu ba a tantance adadin wadanda ke cikin jirgin ba saboda ana ci gaba da aikin ceto.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *