Alfijr ta rawaito shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iso birnin Kano don fara ziyarar aiki a yau Litinin.
Ayyukan da shugaban zai kaddamar a jihar sun hada da.
- kaddamar da wutar lantarki da adadinta ya kai Megawatt 10.
- Kaddamar da tashar tsandauri ta Dala Dry port.
- Kaddamar da cibiyar adana muhimman bayanai ta Kano.
- Kaddamar da kamfanin galaxy backbone.
- Kaddamar da cibiyar yaki da cutar kansa a Asibitin Giginyu.
Shugaban zai kuma ziyarci fadar mai martaba sarkin Kano, sannan ana sa rai zai kaddamar da karin wasu ayyuka daga cikinsu har da babbar gada da gwamnatin Kano ta sanyawa suna Muhammadu Buhari.
Karin Bayani kan ziyarar na nan tafe….
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇