Nadin Farfesa Sani Lawal Kwamishinan Zabe An Dora Kwarya A Gurbin ta – Al’ummar Madobi

IMG 20231224 WA0309

DAGA AMINU BALA MADOBI

Gamayyar Masu ruwa da tsaki na kungiyar rajin cigaban madobi da kewaye sun bayyana nadin Farfesa Sani Lawal Malumfashi kwamishinan zabe KANSIEC amatsayin abin da ya dace.

Alfijir labarai ta rawaito Jagoran tawagar Alh. Buhari Dimi ya bayyana haka yayin da ya ja ayari domin ziyartar sabon Kwamishinan zaben don taya shi murna gameda matsayi da gwamnatin kano ta baiwa dan su.

Alh Buhari Dimi yace tabbas beyi mamaki kan matsayin da aka bashi ba, laakari da irin kyawawan manufofi da tsare tsaren sa na ciyar da kano gaba, kuma a matsayin wanda ya rike kujerar abaya.

Aliyu MUHAMMAD, guda ne cikin ‘yan tawagar, yace babu shakka abin alfahari ne gare su la’akari da duba cantanta da gogewar sa wajan aiwatar da ayyukan sa ga gwamnati.

Anasa jawabin babban mai masaukin baki kuma sabon Kwamishinan zabe Kansiec Farfesa Sani Lawal ya bayyana jin dadi bisa ziyarar ta zumunchi mai cikeda tarihi, inda ya sha alwashin cigaba da karbar shawarwari afannoni da dama domin kaiwa ga nasara.

Farfesan daganan, ya yaba da irin tsari da ‘yan tawagar sukayi na kishin al’umma, inda ya tabbatar da cewa ba zeyi kasa a gwiwa ba wajan yi wa al’umma hidima.

Farfesa Sani Lawal ya godewa Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf bisa nazari tateda duba cancantar sa wajan sake bashi dama a matsayin kwamishinan hukumar zaben karo na biyu.

“Ina godiya mai tarin yawa ga mai girma Gwamna bisa karrama ni, ya girmama ni ya doramin wannan amana mai girma, muna fata allah ya bamu ikon sauke wannan nauyi” Farfesa Sani Lawal.

Tunda farko a jawaban dasuka gabatar dattawan tafiyar Mal. Nura zanta, Mal Urwatu Isah shafa sun ce hakika lamarin ya faranta musu yadda akayi tsare tsare musamman wajan tafiya da dukkan unguwanni 10 na wajen badala, sun kuma yabawa kwamishinan bisa karrama su.

IMG 20231222 WA0078
IMG 20231222 WA0078

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *