NAFDAC Tayi Gargaɗi Kan Wasu Gurbatattun Kayan Abinci Da Ke Yawo A Kasuwanni

“Ba za mu iya yin magana game da amincin abinci da ba a sayar da su a kasuwa ba, saboda ba mu san inda suka fito ba;

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta yi gargadin cewa kayayyakin da suka lalace ko aka sato daga masana’antun abinci, ana shigar da su cikin kasuwanni ta hanyar saka musu leda.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a Lagos ranar Lahadi, ta ce irin wannan ba abin da za a amince da shi bane, domin yana jefa rayuwar masu amfani da su cikin hadari.

Darakta-Janar ta hukumar, Mojisola Adeyeye, ta bayyana haka a taronta na Safety Food and Applied Nutrition Directorate Enagement tare da masu gudanar da harkokin abinci a Legas.

Mrs Adeyeye ta gargadi ‘yan Najeriya kan su kula game da kayan abincin da basu inganci a kasuwa.

“Ba za mu iya yin magana game da amincin abinci da ba a sayar da su a kasuwa ba, saboda ba mu san inda suka fito ba;

Ba za a kuma iya gano ranar ƙarewar su ba,” in ji ta.

A cewar Mrs Adeyeye, a shekarar 2021 da 2022, hukumar ta gudanar da bincike tare da aiwatar da ayyukan a kan hatsin da ba a san su ba, wanda hakan ya sa aka kama mutanen da suke sayar da su ta yanar gizo a Onitsha, aka kawo su Legas.

Ta ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa mutane sun gwammace su sayi kayan da ba a sanyawa tambarin hukumar ba duk da illar da ke tattare da shi.

Shugabar ta kuma bayyana cewa wasu masana’antu na cikin matsalar ta hanyar rashin ingantaccen muhalli.

Ta ce an sace wasu kayayyakin ne a rumbun ajiyar kamfanonin, wasu kuma an debo su ne daga juji da ke Agbara aka sayar wa jama’a.

“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa an zubar da kayayyakin ne ta hannun hukumar kula da sharar ta jihar Ogun.

Hanyoyin zubar da kayayyakin kamfanoni ma na kan kuskure.

“Idan kuna son zubar da wasu lalatattun kayayyaki ko wadanda wa’adinsu suka wuce, to ku lalata su ta hanyar hukumar bincike da tabbatar da doka ta NAFDAC, ba ta hanyar kamfanin kai tsaye ta hanyar hukumomin zubar da shara ba,” inji ta. Ms Adeyeye.

Hakazalika ta yi kira da a gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka kwaso kayayyakin daga wurin da ake jibgewa domin sayarwa.

Ta kuma bukaci masu sarrafa kayayyakin abinci da su kasance cikin saka ido a kodayaushe a kasuwa ta hanyar bin kwakkwafi cikin kasuwanni ko a kamfanoninsu.

Shugabar ta kara da cewa kamfanonin da ba su sanya ido wajen inganta kayayyakinsu ba to za a dauki mataki akansu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *