Najeriya ta kaddamar da shirin ba da tallafin kudi ga magidanta miliyan 15

FB IMG 1693849912844

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi ga magidanta miliyan 15, wanda hakan na cikin manufofinsa da aka yi wa laƙabi da ‘kyakkyawan fata’.

Alfijir Labarai ta rawaito Tinubu ya kaddamar da shirin ne a yau Talata a bikin ranar kawo karshen talauci ta duniya, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Tinubu ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume yayin kaddamar da shirin.

A jawabinsa na bikin samun ƴancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 2023, shugaban ya sanar da cewa shirin ba da tallafin kuɗin, zai fi mayar da hankali kan taimakawa marasa galihu.

Magidantan da iyalansu sun kai yawan ƴan Najeriya miliyan 62, a cewar ministar ba da agaji, Betta Edu.

Ta ce za a bai wa kowane magidantci naira 25,000 har na tsawon wata uku, wanda ya kai naira 75,000.

Ministar ta kuma ce nan ba da jimawa ba, za a kaddamar da wani tsarin ba da tallafi mai suna ‘Iya Loja Funds’ wanda zai samarwa masu ƙananan sana’o’i bashin naira 50,000 kowanne.

Waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da ministar ma’aikatar ba da agaji rage talauci Dr Betta Edu, ministan kuɗi, Wale Edun, wakilin bankin duniya na ƙasashe, Shubham Chaudhuri, shugaban ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Matthias Schmale da sauran manyan baki

BBC .

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *