Juyin Mulki Nijar! Babban abin da ya sa muka ƙi sakin Mohammed Bazoum – Tchiani

FB IMG 1702359002916

Jagoran sojojin da suka hambarar da gwamnatin dimokradiyya a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ce akwai dalilan da suka sanya su ƙin sakin hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum.

Alfijir labarai ta rawaito Janar Tchiani ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta gwamnati a ranar Lahadi.

Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas ko Cedeao) ta ce za ta wakilta wani ayari da zai ƙara tattaunawa da jagororin mulkin sojin na Nijar domin warware kiki-kaka da ake ciki tun bayan juyin mulkin watan Yuli.

Tun farko, Ecowas ta yi barazanr ɗaukar matakin soji a kan Jamhuriyar Nijar matuƙar sojojin suka gaza mayar da Bazoum kan mulki.

Sai dai sojojin sun ƙi bin umarnin, lamarin da ya sa ƙungiyar ta ƙi cire takunkuman da ta ƙaƙaba wa Nijar tun da farko.

Sai dai a tattaunawar da ya yi da kafar yaɗa labarai ta RTN, Shugaba Tchiani ya nuna cewa rashin tsaro da rashin tabbas na cikin dalilan da suka sa sojoji ƙin sakin hamɓararren shugaban.

A cewarsa: “Mu mun san abin da ya sa muke tsare da shi.”

Tchiani ya ce ba zai yiwu a saki Bazoum a lokacin da ƙasashen duniya ke ta kiraye-kirayen a sake shi ba, saboda barazana ta tsaro.

Ya ƙara da cewa har yanzu Nijar na cikin barazanar fuskantar hari: “Muna cikin barazanar (kawo mana) hari, muna bisa barazanar ta’addanci”.

Ba ta yiwuwa in bar shi ya fita, (idan) lokaci idan ya yi na fitar shi, zai fita.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

One Reply to “Juyin Mulki Nijar! Babban abin da ya sa muka ƙi sakin Mohammed Bazoum – Tchiani”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *