
Alfijr ta rawaito Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kammala shirin naɗa tsohon gwamnan Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, da kuma Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakin sa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Akpabio da Barau na cikin ƴan takara 9 da ke neman shugabancin majalisar dattawa, wanda za a rantsar da su a ranar 13 ga watan Yuni.
Sahihan majiyoyi sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa tuni Tinubu ya sanar da Akpabio da Barau wannan ƙuduri nasa a wata ganawar sirri da su ka yi a Abuja bayan dawowarsa daga ƙasar Faransa, inda ya shafe kwanaki 34 a can.

Majiyoyin sun tabbatar wa da Daily Trust cewa a yayin ganawar, wacce dama sabo da Barau a ka yi, Tinubu ya rarrashe shi da ya hakura da takarar shugabancin majalisar dattawa domin a samu adalci da daidaito na addini a shugabancin ƙasar.
A cewar majiyoyin, Tinubu ya nunawa Barau cewa ya matuƙar cancanta da ya zama shugaban majalisar dattawa, to amma kasancewar Tinubu da mataimakin sa Kasim Shettima musulmai ne, ya kamata a ce Barau ya ajiye burin nasa ya baiwa kirista dan kudu dama domin a samu daidaito da kuma zaman lafiya a mulkin ƙasar.
“A ƙarshen ganawar ne sai Tinubu ya shaidawa Barau cewa yana don ya zama mataimaki ga Akpabio su yi aiki tare,” in ji majiyoyin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ