NJC ta amince da ƙarin girma ga alkalin da ya yanke hukuncin zaɓen gwamnan Kano a kotun daukaka kara

IMG 20231207 150008

Hukumar Kula da Fannin Shari’a ta Ƙasa, NJC ta amince da ƙarin girma zuwa alkalancin kotun koli ga Moore Aseimo A. Adumein, alkalin da ya yanke hukuncin zaɓen gwamnan Kano mai cike da rudani.

Alfijir labarai ta rawaito wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na NJC, Soji Oye, an amince da ƙarin girma ga Adumein, duk da kuskure da aka tafka a shari’ar, wanda bayan ya yanke cewa kotun ta tabbatar da hukuncin tirabunal, wanda ya tabbatar da nasar Nasiru Gawuna, sai kuma da kundin hukuncin ya fito, sai aka ga ashe asali korar hukuncin tirabunal din kotun ta yi.

Oye ya ce za a rantsar da alkalami da aka yi wa ƙarin girma bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da majalisar Dattawa sun amice.

Ya ce sauran shugabannin kotuna da aka yi wa ƙarin girma, za a rantsar da su ne bayan gwamnonin jihar da majalisar jihar su sun tantance da amincewa da su.

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *