Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa a ranar Lahadi 15 ga Satumba za a soma lodin kashi na farko na man fetur daga matatar mai ta Dangote da ke Jihar Legas.
Alfijir Labarai ta rawaito kwamitin shugaban kasa kan sayar da ɗanyen mai ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a a Abuja.
Shugaban hukumar tattara haraji na Najeriya Zach Adedeji wanda mamba ne a kwamitin ya bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Oktoba, kamfanin na NNPCL zai soma bayar da ganga 385 ta ɗanyen mai a kullum ga matatar Dangote.
Ya ƙara da cewa ita kuma matatar ta Dangote za ta bayar da fetur da man dizel wanda ya zo daidai da darajar man a kasuwa kuma a biya kuɗin a naira.
An shafe lokaci ana kwan-gaba kwan-baya tsakanin kamfanin na NNPCL da kuma matatar ta Dangote dangane da batun ciniki da hada-hada ta ɗanyen mai.
Duk wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu ƙarin kuɗin mai a Nijeriya, lamarin da ya ƙara saka ‘yan ƙasar da dama ƙorafi.
A farkon watan nan ne aka wayi gari gidajen mai mallakar kamfanin na NNPCL sun ƙara farashin da ake sayar da man fetur ɗin. OSai dai jama’a da dama a faɗin ƙasar na fata za a samu sauƙin farashi idan matatar ta Dangote ta soma samar da man fetur a ƙasar.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj