A cikin hirar, mun ga inda wanda ake zargin ya yaudari marigayin da maganar luwadi tare da nuna masa hotonsa tsirara.
Alfijir Labarai ta rawaito Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC a Bauchi ta kama wani dalibin jami’a da laifin daba wa wani yaro dan shekara 17 wuka ya kashe shi har lahira a karamar hukumar Misau ta jihar.
Kwamandan hukumar, Ilelaboye Oyejide, wanda ya tabbatar da kamen a ranar Lahadi a Bauchi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 20 ga Oktoba, 2023.
Ya ce rundunar ta samu labarin cewa an tsinci gawar wani dalibin makarantar sakandare mai suna Umar Usman a nannade, kuma an jefar da shi cikin farin kyalle a gefen Misau.
“Ba tare da bata lokaci ba aka kai shi babban asibitin Misau, inda aka tabbatar da cewa ya mutu kuma aka mika shi ga ‘yan uwa don yi musu jana’iza.
“Wannan lamari ne na kisan gilla,” in ji Oyejide, ya kara da cewa rundunar ta tura jami’an leken asiri zuwa Misau domin gudanar da bincike tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
“Bayan bincike da jami’an suka yi, an kama wani Abdullahi Ibrahim, dalibi mai mataki label 500 a fannin likitancin dabbobi na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
“Mun fahimci cewa akwai wata tattaunawa ta sadarwa tsakanin wanda ake zargin da marigayin.
“A cikin hirar, mun ga inda wanda ake zargin ya yaudari marigayin da maganar luwadi tare da nuna masa hotonsa tsirara.
“Lokacin da mamacin ya je ya same shi ko ta yaya aka caka masa wuka a ciki, kuma an nade shi da farin kyalle aka jefar da shi inda aka same shi,” in ji shi.
A cewar Oyejide, za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.
(NAN)
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ