Ofishin Jakadancin ƙasar Amurka a Abuja ya yi gargadi ga ‘yan ƙasar Amurka da ke Najeriya kan yiwuwar ɓarkewar zanga-zanga a Abuja, sakamakon ƙarin tashin hankalin da ke tattare da rikicin Amurka/Isra’ila da Iran a gabas ta tsakiya.
A cikin sanarwar da ya wallafa a dandalin X, ofishin ya ce akwai yiwuwar zanga-zanga mai ƙarfi a babban birnin ƙasar, tare da shawartar ‘yan Amurka da su zauna a gidajensu a ranar Laraba, 4 ga Maris.
Sanarwar ta kuma buƙaci su guji wuraren taron jama’a, su riƙa lura da muhallinsu, tare da bibiyar kafafen yaɗa labarai domin samun sabbin bayanai.
Duk da gargaɗin, ofishin jakadancin ya tabbatar da cewa sashen ba da biza da kula da al’amuran ‘yan ƙasa a Abuja da Legas na ci gaba da aiki kamar yadda aka saba.
Daily Nigerian
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t