Ramadan! Gwamnati Ta Ayyana Hutun Kwana Biyar Ga Jama’a

IMG 20240311 WA0047

Ta yi kira ga ma’aikatan da farar hula da masu rike da mukaman siyasa da su dauki wannan aiki a matsayin kira na yi wa al’umma hidima

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnatin jihar Neja ta ayyana mako mai zuwa daga Litinin zuwa Juma’a a matsayin ranar hutu don sa ido da rarraba kayan abinci da ciyar da watan Ramadan.

Gwamnan a cikin sakon ya bayyana cewa za a raba kayayyakin jin kai a fadin jihar domin dakile illar da tattalin arzikin kasar ke yi wa jama’a.

A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishiniyar yada labarai Honorabul Binta Mamman, ranar hutun jama’a ne domin baiwa ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa damar shiga rabon kayan agaji da kuma ciyar da watan Ramadan a kananan hukumominsu daban-daban.

Ta yi kira ga ma’aikatan da farar hula da masu rike da mukaman siyasa da su dauki wannan aiki a matsayin kira na yi wa al’umma hidima tare da yin kira ga jama’a da su ba jami’ai hadin kai da kuma kasancewa cikin tsari a duk wuraren rabon abinci da ciyarwa domin gudanar da aikin cikin nasara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *