Rashin Imani! Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Jariri Dan Wata 4

FB IMG 1709368775063

Maharan sun kutsa har cikin uwar dakin ma’aurata suka dora musu bindiga a kai, sannan suka kwace jaririn suka tsere

Alfijir labarai ta rawaito ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani jariri dan wata hudu da haihuwa a Jihar Akwa Ibom.

Da misalin karfe 3 na daren Asabar ne wasu ’yan bindiga biyu suka kutsa cikin gidan wani magidanci mai suna Mista Edeme Eyo suka kwace jaririn nasu.

Mista Edeme Eyo ya ce maharan da suka zo dauke da bindigogi da adduna sun kuta shar cikin uwar dakinsu ne suka dora musu bindiga a kai da matarsa, suka nemi a ba su jaririn.

A cewarsa, ’yan bindigar sun fi karfinsa, matarsa tana ihu, amma suka kwace jaririn daga hannunta suka shiga wata mota da suka zo da ita suka tsere.

Sojojin Nijar sun kama jagoran ’yan bindigar Najeriya
Najeriya ta karyata batun bude sansanin sojin kasar waje
Magidancin ya ce wannan abin ya faru ne ba da jimawa ba da ya rasa dansa na fari, wanda ya rasu ’yan watanni bayan haihuwarsa.

Iyayen jaririn da ke zaune a kauyen Enen-Atai da ke Karamar Hukumar Itu sun roki jami’an tsaro su taimaka su ceto musu jaririn nasu daga hannun maharan.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Akwa Ibom, ASP Timfon John, ya ce rundunarsu tana kokarin kamo ’yan bindigar da kuma ceto jaririn don mika shi ga iyayensa.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *