Rikicin APC A Kano: Yadda Ta Kasance A Kotun Koli A Yau Alhamis Tsakanin Dan Zago Da Abdullahi Abbas

Alfijr ta rawaito kotun Koli ta tanadi hukunci kan karar rikicin APC na Kano.

Idan za a iya tunawa, wata babbar kotun tarayya Abuja, a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2021, ta bayyana zaben gundumomin da bangaren gwamna Abdullahi Ganduje ya gudanar a Kano, ba bisa ka’ida ba.

ALFIJR

Hakazalika, a ranar 17 ga watan Disamba, kotun karkashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu ta amince da zaben kananan hukumomin da bangaren Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya gudanar. Da rashin gamsuwa da hukuncin, bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ya shigar da kara a kotun daukaka kara da ta soke hukuncin da karamar kotu ta yanke wanda ya baiwa bangaren Sanata Ibrahim Shekarau G-7 na jam’iyyar APC nasara, a ranar 17 ga Fabrairu 2022.

A ranar Alhamis, mutum biyar din. Kotun koli karkashin jagorancin mai shari’a Mary Peter Odili ta dage zaman tare da ajiye hukunci bayan amincewa da bayanan dukkan bangarorin da ke cikin karar.

ALFIJR

Lauyan ya gabatar da korafin farko ga wadanda suka amsa na daya da na biyu da na uku, wato All Progressive Congress, Mai Mala Buni da John James Akpanudoedehe, bi da bi, Barr. Abdul Adamu Fagge da yake kalubalantar sauraron karar da cewa daya daga cikin buƙatun masu daukaka kara na da alaka da wakilan jam’iyyar na kasa zuwa babban taron jam’iyyar lamarin da ya riga ya. gudana

Slide Up
x