Rundunar Yan Sanda Nigeria Sun Kashe ’Yan Bindiga 2 A Garin Kaduna

Rundunar Yan Sanda Nigeria Sun Kashe ’Yan Bindiga 2 A Garin  Kaduna.

Best Seller Channel

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana yadda ta halaka wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne guda biyu a kauyen Riheyi da ke karamar hukumar Giwa Jami’in hulda da jama’an rundunar na jihar Kaduna. 
ASP Mohammed Jalige, ya bayyana hakan ta wata takarda da rundunar ta saki a ranar Talata a Kaduna 

Best Seller Channel 
ASP Jalige, ya Kara da cewa a ranar Litinin da misalin karfe 4:30pm lamarin ya faru, inda ya ce sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan.
Jalige ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Mudassiru Abdullahi, ya jinjina wa jami’an rundunar kan kokarin dakile ’yan bindiga da suka yi.
Kwamishinan ya umarci ’yan sandan jihar da su ci gaba da dagewa wajen bankado maboyar bata-gari da ke fadin jihar.
Best Seller Channel 
Ya kara da cewa, sakamakon karatowar lokacin bukukuwan karshen shekara, yana da kyau jama’a su sanya ido sosai tare sa taimaka wa jami’an tsaro wajen samun nasara a ayyukansu.

Slide Up
x