Rundunar yan sanda a Abuja, babban birnin Nijeriya ta ce ta kai samame wata matattarar miyagu inda ta kama mutum dari uku da bakwai da ake zargi da aikata laifuka.
Alfijir labarai ta rawaito Kwamishinan yan sanda a Abuja, CP Benneth C. Igwe ne ya jagoranci tawagar rundunar ‘Operation Velvet’ wajen kai samame kan matattarar da ke Gidan Dambe a yankin Dei-Dei zuwa Zuba.
Yayin binciken, an gano bindiga daya da alburusai goma sha biyar a hannun wani da yake ikirarin shi jami’in hukumar tsaro ta farin kaya ne.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta wallafa a shafin X, sauran kayayyakin da aka gano sun hada da babura da kunshin tabar wiwi da haramtattun kwayoyi da ake zargi mutanen sun sace ne daga hannun mutanen da ba su ji ba su gani ba.
Kwamishinan yan sandan ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen da aka kama.
A makon da ya gabata ne aka kaddamar da rundunar ta musamman domin kawo karshen duk wasu miyagun laifuka a Abujar.
Kwamishinan ya kuma gargadi yan sanda kan tatsar jama’ar sannan su nuna kwarewa wajen aiwatar da ayyukansu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V