Duk Girman Gona! Hisbah Ta Cafke Murja Ibrahim Kunya A Kano

FB IMG 1707813188222

Hukumar Hisba ta samu nasarar damke jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya a Kano.

Alfijir labarai ta rawaito Hukumar Hisbah ta kama Murja Kunya ne biyo bayan ci gaba da yin abubuwan rashin da’a da suka saba da koyarwar addinin Musulinci.

Idan zaku iya tunawa a baya an yi mata nasiha tare da lura da irin abubuwan da ta ke aikata a shafukan sada zumunta sai dai ba ta canja halin. ba.

Jarumar Tiktok din dai ta shahara, wajen furta kalaman batsa da na rashin tarbiya da kuma sanya sutura da ta saba wa addinin musulinci da al’adar Hausawa tare da kwaikwayon wasu al’adu na daban.

Tun a baya dai jama’a da dama ke ganin beken hukumar Hisbar na kin kama Murja Kunya sakamakon yadda ta shafa wa idon ta da toka, ta ke aikata badala a shafukan sada zumunta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

One Reply to “Duk Girman Gona! Hisbah Ta Cafke Murja Ibrahim Kunya A Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *